1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages
  • Afirka ta kudu na neman kofi karo na biyu

    Rukunoni na gasar kwallon kafar Afirka a 2013

    Afirka ta kudu na neman kofi karo na biyu

    Bayan da Libya ta fada cikin rikici, hukumar kwallon kafa ta Afirka ta amince Afirka ta kudu ta daukin bakwancin gasar 2013. Wannan zai iya zama wata dama ga "Bafana Bafana" ta lashe kofin karo na biyu a gida kamar yadda ya faru a 1996. Afirka ta kudu ta zama saniyar ware lokacin da kasar ta yi fama da Apartheid. Afirka ta Kud na rukunin A da ita da Angola, da tsibirin Cap Verd da kuma Moroko.

  • Zambiya na neman kare kafin 2012

    Rukunoni na gasar kwallon kafar Afirka a 2013

    Zambiya na neman kare kafin 2012

    Ba wanda zai manta da ba wa marada kunya da kungiyar Zambiya ta yi a gasar kwallon kasashen Afirka na 2012. A bugun daga kai sai mai tsaron da ya gudana bayan kara mintuna 30, kungiyar ta Kasar Zambiya ta doke Côte d' Ivoire de ci 8:7. Ga Zambiya dai, wannan shi ne karo na biyu da ta taba lashe kofin na Afirka. Kasar za ta yi wasanninta ne a rukunin C tare da Nigeria da Burkina Faso kuma Habasha.

  • Côte d'Ivoire ba ta so a doke ta a wasan karshe

    Rukunoni na gasar kwallon kafar Afirka a 2013

    Côte d'Ivoire ba ta so a doke ta a wasan karshe

    Su "les Elephants" za su je Afirka ta kudu a matsayin wadanda suka zo na biyu a gasar Karshe.Ci 4:2 Côte d'Ivoire ta doke Senegal a matakin farko a Abidjan. Sai dai tashin hankali da aka fiskanta a mataki na biyu a Dakar ya sa a dakatar da wasan, kana aka bayyanata a matsayin wacce ta kai labari . Côte d'Ivoire za ta yi wasanninta a rukunin D da Tunesiya da Algeriya da kuma Togo.

  • Angola na fatan taka rawar gani a gasar

    Rukunoni na gasar kwallon kafar Afirka a 2013

    Angola na fatan taka rawar gani a gasar

    Wannan shi ne karo na bakwai da Angola ta cancanci shiga gasar kwallon kafa na kasashen Afirka. Nasarar da 'yan wasan "Palancas Negras" suka samu akan takwarorinsu na Zimbabwe ne ya ba su damar zuwa Afirka ta Kudu. Bayan da aka doke su da ci 1:3, 'yan wasan na Angola sun doke na Zimbabwe da ci 2:0 a gida. Za ta yi wasanninta ne a rukunin na A tare da Afirka ta kudu da Moroko da kuma Cap Verde.

  • Kwarin guywa na magoya bayan Angola

    Rukunoni na gasar kwallon kafar Afirka a 2013

    Kwarin guywa na magoya bayan Angola

    Magoya bayan Angola sun bayyawa wa DW cewa kungiyarsu za ta ba wa marada kunya a rukuninta a inda za ta haye mataki na gaba. Suka ce ba doke Afirka ta Kudu da Moroko ba wani abu ne mai walan gaske ba Mai horas da Angola Gustavo Ferrín,wanda ya fito daga Urugay ya ce wadanda ke cikin rukinin A ba kanwar lasa ba ne.

  • Sabon shiga da suka fito daga Cap Verd

    Rukunoni na gasar kwallon kafar Afirka a 2013

    Sabon shiga da suka fito daga Cap Verd

    Tsibirin Cap Verde da ke yammacin Afirka na alfahari da kungiyar kwallon kafar ta. Wannan shi ne karon farko da ta ke shiga matakin karshe na wasannin kasa da kasa. Ta cika burinta ne sakamakon nasarar da ta samu akan kungiyar kasar Kamaru. Ranar 19 ga janairu za ta yi wasanta na farko da Afirka ta kudu mai masaukin baki a birnin Johannesbourg.

  • Lúcio Antunes: Uban gayya na Cap Verd

    Rukunoni na gasar kwallon kafar Afirka a 2013

    Lúcio Antunes: Uban gayya na Cap Verd

    Kasar Cap Verde ta cire wa kanta kitse a wuta karkashin mai koyarwa Lúcio Antunes . Ta doke "Indomitables Lions " na Kamerun a matakin farko a Praia da ci 2:0. Doke ta da Kamaru ty yi da ci 1:2 a Yawunde baui hana ta kai labari ba. Kap Verd za ta yi wasannnta ne a rukunin mutuwa na Ainda za ta kara da Morokko da Afirka ta kudu da kuma Angola.

  • Kasar Ghana na neman kofi na biyar

    Rukunoni na gasar kwallon kafar Afirka a 2013

    Kasar Ghana na neman kofi na biyar

    So hudu Ghana ta lashe kofin kwallon kafa na Afirka. Ta kai ga buga wasan karshe so takwas. Karonta na karashe shi wanda ya gudana a angola a 2010. Sai dai a wannan karon GHana ba ta kai labari ba a gaban Masar 0:1. Daya daag cikin shaharurrun 'yan wasanta shi André Ayew (dama) wanda ke bugawa a Marseille. Ghana za ta buga ne rukunin B da Mali, da Nijar da kuma jamhuriyar demokaradiyar Kwango.

  • Najeriya na nuna bajinta a ko wani lokaci

    Rukunoni na gasar kwallon kafar Afirka a 2013

    Najeriya na nuna bajinta a ko wani lokaci

    "Super Eagles" na daga cikin kungiyoyin kwallon kafa da suka fi fice a Afirka. A shakarar 1994 FIFFA ta ta sanya ta a matsayi na biyar na kasashe da suka fi shahara a duniya a fagen tamaula. Har yanzu ta na ci gaba da amsa sunan manyan dawa na kasashen Afirka. A shekarun 1980 da 1994 Najeriya ta lashe kofin Afirka. Yayin da a wasanni 2002, da 2004 da 2006 da 2010 ta samu matsayin na uku.

  • Mali za ta je da takaici na 'yan tawaye

    Rukunoni na gasar kwallon kafar Afirka a 2013

    Mali za ta je da takaici na 'yan tawaye

    A fannin siyasa Mali na cikin hali na tsaka mai wuya sakamakon karbe ikon arewacin kasar da masu kaifin kishin addini suka yi. Amma kuma bai hana cancantar shiga wasannin karshe na neman lashe kofin kwallon kafa da za su gudana a Afirka ta Kudu ba. A gasar da Equatorial-Guine da Gabon suka dauki bakwanci, ita ce ta zo ta uku ba tare da zato ko tsammani ba.

  • Burkina Faso na so ba wa marada kunya

    Rukunoni na gasar kwallon kafar Afirka a 2013

    Burkina Faso na so ba wa marada kunya

    Burkina Faso da ke yammacin Afirka ba ta cikin rukunin kasashe da kwallon kafa ya samu karbuwa sosai a cikinsu. Bajintar ta ita matsayi na hudu da ta samu a wasannin da suka gudana a shekarar 1998. Amma dai tun 1996 aka damawa da Burkina Faso akai akai a Faso a gasannin Afirka. Dan wasanta na gaba Moumouni Dagano (hoto) da ke bugawa a Al-Sailiya na Qatar na daga cikin wadanda ta fi ji da su.

  • Tunisiya: 'yar gida a gasar kwallon Afirka

    Rukunoni na gasar kwallon kafar Afirka a 2013

    Tunisiya: 'yar gida a gasar kwallon Afirka

    So 15 Tunisiya ta shiga wasannin karashe na neman lashe kofin Afirka. A shekara ta 2004 ta dauki bakwancin wasannin. A shekarar 1978 ne ta rubuta tarihinta inda ta doke Mexico da ci 3:1 a wasannin kwallfon kafa na duniya a Argentina. Wannan dai shi ne karon farko da wata kungiyar da ta fito daga nahiyar afirka ta samu nasara akan wata kungiya a wasan kwallon kafa na duniya a cikin tarihi

  • Moroko: Zakunan Atlas

    Rukunoni na gasar kwallon kafar Afirka a 2013

    Moroko: Zakunan Atlas

    Doke Mozambik da kungiyar "Zakunan Atlas" ta Moroko ta yi da ci 4:0 a birnin Mararakech ne ya ba ta damar shida a dama da ita a Afirka ta kudu. Moroko ce a 1986 ta zama kasar farko ta Afirka da ta taba kai wa takabi na gaba a wasanni neman lashe kofin duniya bayan da ta wasanninta da Ingila da Polond da kuma portugal. A 1976 kasar ta larabawa ta lashe kofinta na kwallon Afirka.

  • Nijar: Karo biyu ke nan ta na cancanta

    Rukunoni na gasar kwallon kafar Afirka a 2013

    Nijar: Karo biyu ke nan ta na cancanta

    Bayan shekara ta 2012 a Afrika ta Kudu, wannan shi ne karo na biyu da kungiyar "Menas" ta Jamhuriyar Nijar ke shiga gasar kwallon kafa ta kasashen nahiyar Afirka. Dan wasanta na baya Mohamed Chicoto (hoto) wanda ya ke bugawa a AS Marsa ta Tunesiya na daya daga cikin fitattun 'yan wasa da Nijar za ta dogara a kansu wajen cimma biyan bukata.

  • Togo: Kungiyar da ta farfado daga hari

    Rukunoni na gasar kwallon kafar Afirka a 2013

    Togo: Kungiyar da ta farfado daga hari

    So shida Togo ta shiga gasar kwalon Afirka a tarihinta. Hakazalika a shekara ta 2006, an fafata da ita a kofin duniya na kwalon kafa da Jamus ta dauki bakwanci. A shekara ta 2010 jim kadan kafin fara wasannin Afirka a Angola, kungiyar kasar ta fiskanci hari daga 'yan tawaye da ke neman dara kasar gida biyu, ind mutane uku suka mutu.

  • Babban kalubale na kasar habasha

    Rukunoni na gasar kwallon kafar Afirka a 2013

    Babban kalubale na kasar habasha

    Kasa da shekara guda na aiki tukuru mai horaswa Sewnet Bishaw ya shafe wajen shigar da Habasha rukunin wadanda za su buga a Afirka ta Kudu. Shekaru 31 Ethipiya ta share ba tare da halartar wasannin karashe na neman lashe kofin kwallon Afirka ba. A shekarar 1962 ta taba lashe kofin lokacin da Ethipiya da ke gabashin Afirka ta dauki bakwancin wasannin na Afirka.

  • Kwongo: Magadan fitattun 'yan kwallo

    Rukunoni na gasar kwallon kafar Afirka a 2013

    Kwongo: Magadan fitattun 'yan kwallo

    A 1974 kasar da a da ake kira Zaire ta taka rawar gani a fagen kwallon kafa: Ita ce kungiyar farko ta kasashen Afirka da ke kudu da Sahara da ta fara cancantar shiga wasannin karshe na neman lashe kofin kwallon kafa na duniya. Ya zuwa yanzu dai kungiyar Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango ta lashe kofin Afirka so biya a tarihinta: a shekarar 1968 da kuma shekarar 1974.


    Mawallafi: essôa, Marcio / Beck, Johannes | Edita: Mouhamadou Awal

SHIRYE-SHIRYE

Rediyon DW koyaushe a cikin kunne

ALBISHIR: Kuna iya sauraron shirye-shiryen DW a harsunan Afirka guda shida kai tsaye (hausa, swahili, amharik, ingilishi, faransanci, harshen Portugal) a duk lokutan da aka saba. Idan sun wuce ku, kuna iya sauraren shirye-shiryen Hausa ta „Audio on demand“! Kuna iya zaben abin da za ku saurara daga jerin shafunan dake kasa.

Kuna iya tuntuɓarmu akan wannan adireshi: hausa@dw.de ko kuma ku aiko mana da gajeren saƙo akan wayarmu mai lamba: +49-173-7100428