1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages
Wrong language? Change it here. DW.DE has chosen Hausa as your language setting.
  • Fußballstar Didier Drogba bei der Champions-League-Siegerehrung 2012
(Foto: REUTERS/Dylan Martinez)
(GERMANY - Tags: SPORT SOCCER)

    Taurarin ‘yan wasan Afirka

    Didier Drogba, sanannen dan kwallo....

    Baya ga bajintar da su ke nunawa, suna kuma taimakon wasu. Galibin taurarin kwallon Afirka, na zama abin koyi ne a kasashensu na asali. Daya daga cikinsu kuwa shi ne Didier Drogba, wanda a halin yanzu ke kungiyar Galatasaray Istanbul. A 2012 ya ci gasar Champions League da Chelsea. Ya kuma sanya tutar kasarsa a kafadarsa yayin bukin karbar lambar yabon.

  • Mann liest ivorische Zeitung auf der Didier Drogba zu sehen ist.
(Foto: AFP PHOTO/ SIA KAMBOU)
(Photo credit should read SIA KAMBOU/AFP/Getty Images)

    Taurarin ‘yan wasan Afirka

    …kuma abin koyi ne

    Sa’ilin da zaben shugaban kasa na Cote d’Ivoire ya janyo rigima da zubar da jini a kan tituna, Didier Drogba ya kaddamar da gangamin fadakarwa ta gidajen jaridu ta hanyar baiwa rigima jan kati. Ya kuma garzaya Jamus domin goyon bayan kirkiro da asusun agaji ga mabukata a bukin ban-kwana ga Michael Ballack a Leipzig, ranar 05.Juni 2013.

  • Marathon-Läufer Wesley Korrir beim Einlauf ins Ziel.
(Foto: Photo by Jim Rogash/Getty Images)

    Taurarin ‘yan wasan Afirka

    Dan gudun tsere kuma dan siyasa

    Wesley Korrir, dan wasan guje-guje ne da ke da ra’ayin Siyasa. Shi ne zakaran tsere na Boston a 2012, kuma an zabe shi mukaddashin shugaban majalisar dokokin Kenya a watan Maris na 2013, kana yana wakiltar Cherangani. Amma ban yi watsi da harkar wasa ba. An dama da shi a tseren Boston na bana in da ya zo na biyar gabannin hare-haren da suka dakushe armashin gasar.

  • Verstorbener Basketballstar Manute Bol hält eine Rede vor Demonstranten.
(Foto: Photo by William Thomas Cain/Getty Images)

    Taurarin ‘yan wasan Afirka

    Daya daga cikin fitattun 'yan wasan kwando

    Marigayi Manute Bol ya rikida zuwa dan siyasa. Fitaccen dan wasan kwallon kwandon, wanda tsawonsa ya kai mita 2 da centimita 31 ya yi Allah wadai da yakin da a ke yi a kasarsa Sudan sa’ilin jerin gwanon da a ka yi a Philadelphia. Ta hanyar gidauniyarsa ta Ring True, ya tattara agaji ga ‘yan gudun hijirar Sudan. A yanzu gidauniyar na taimakon sha’anin ilimi ga ‘yan wasan Afirka.

  • (Foto:

    Taurarin ‘yan wasan Afirka

    Mace mai kamar maza a fagen wasannin Afirka...

    Ba za a taba mantawa da Nawal El Moutawakel, ‘yar kasar Morokko ba. A gasar Olympic na 1984 a Los Angeles, ta zama zakara a tseren mita 400, inda ta zama mace Musulma ‘yar Afirka da ta fara lashe lambar zinare a gasar Olympic.

  • Brasiliens Fußballlegende Pelé und die ehemalige marokanische Läuferin Mawel El Moutawakel.
(Foto:AP Photo/Ricardo Moraes)

    Taurarin ‘yan wasan Afirka

    ...daga nan kuma sai ta fara aiki da Kwamitin Olympic na duniya

    Shekaru 29 bayan haka, Nawal El Moutawakel, ta zama mataimakiyar shugaban Kwamitin Olympic na Duniya. Tana kuma taka rawar gani wajen shirya gasar Olympic ta 2016 a Rio kuma ta gana da Pele, shahararren dan wasan kwallon kafar Brazil. Har yanzu El Moutawakel shahararriya ce a kasarta ta gado Morokko.

  • Bildergalerie Sportler aus Afrika - Roger Milla

    Taurarin ‘yan wasan Afirka

    Cin kwallo wa Kamaru...

    Shahararren dan wasan Roger Milla ya yi bajinta a gasar cin kwallon kafa ta duniya ta 1990 a Italiya. Kwallon da ya ci ya sa Kamaru zama kasar Afirka ta farko da ta tsallake zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya. Ya yi rawa bayan duk wani kwallon da ya ci.

  • (Foto:)

    Taurarin ‘yan wasan Afirka

    ...yana kuma taimaka wa wasu

    Roger Milla na amfani da shahararsa wajen goyon bayan ayyuka na-gari. A 2001, ya zama dan Afirka na farko da a ka zaba a matsayin jakada ga hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke yaki da cutar AIDS.

  • Bildergalerie Sportler aus Afrika - Maria de Lurdes Mutola

    Taurarin ‘yan wasan Afirka

    Taimaka wa na baya

    ‘Yar wasan guje-guje da tsalle-tsallen da ta yi fice a tseren mita 800, Maria de Lurdes Mutola ta lashe zinare a gasar duniya sau uku da kuma a Olympic. A kasarta Mozambik kuwa, tana taimaka wa matasa da ke da basira ta fannin wasa ta hanyar gidauniyarta mai suna Lurdes Mutola, kana tare da tallafin UNICEF, tana shawo kan Iyaye su yi wa ‘ya’yansu riga-kafin cutar shan-Inna da kyanda.

  • (Foto: (Photo credit should read DENIS CHARLET/AFP/Getty Images)

    Taurarin ‘yan wasan Afirka

    Wani hanin ga Allah baiwa ce

    A birnin Salt Lake a 2002, Isaac Menyoli ya zama dan wasan Kamaru na farko da ya shiga aka dama da shi a gasar tseren kankara. Shi ne kashin baya a gasar ta kilomita 15. Sai dai bai shiga da niyyar zama zakara ba, amma don ya janyo hankula ga cutar AIDS a kasarsa. Ya yi hakan ne ta hanyar hira da manema labarai jim kadan bayan gasar, wadda in ba don Olymypics ba, da bai sami wannan dama ba.


    Mawallafi: Nadina Schwarzbeck / Saleh Umar Saleh | Edita: ZMA

SHIRYE-SHIRYE

Rediyon DW koyaushe a cikin kunne

Kuna iya sauraron shirye-shiryen DW a harsunan Afirka guda shida kai tsaye (Hausa da Swahili da Amharik da Ingilishi da Faransanci da kuma harshen Portugal) a lokutan da aka saba. Idan shirye-shiryen Hausa sun wuce ku, kuna iya sauraronsu ta "Audio on demand“ ta hanyoyin da muka yi muku tanadi a ƙasa.

Kuna iya tuntuɓarmu a kan wannan adireshi: hausa@dw.de ko kuma ku aiko mana da gajeren saƙo a kan wayarmu mai lamba: +49-173-7100428.

Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Kano- Muryar Jama'a

Freedom Radio- Muryar Jama'a