1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages
  • Cibiyar addinin Musulunci

    Aikin Hajji a Makkah

    Cibiyar addinin Musulunci

    Burin kowane Musulmi shi ne ya tafi Makkah, domin a nan ne Ka'aba wato ɗakin Allah ya ke. Ka'aba na tsakiyar masallacin Harami kuma ana lulluɓe ta da baƙin zane da ake kira kiswa. Kowane Musulmi da ya tafi aikin Hajji ya na kewayeta sau bakwai wato ɗawafi.

  • Tafiya mai hatsari

    Aikin Hajji a Makkah

    Tafiya mai hatsari

    A zamanin da Mahajjata na tafiya Makkah a ƙasa ko a kan raƙumma. A kan kai wa Musulman hari a kan wannan hanya mai tsawo daga Masar ko daga wasu ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya zuwa Makkah.

  • Sauƙin tafiya

    Aikin Hajji a Makkah

    Sauƙin tafiya

    A wannan zamani da muke ciki akasarin Mahajjata su na zuwa Saudi Arabiya ta jiragen sama. Daga filin jiragen sama na ƙasa da ƙasa dake birnin Jeddah, motocin bas-bas na ɗaukar Mahajjata zuwa birnin Makkah mai tazarar kilomita 80.

  • Gari mai cike da tantuna

    Aikin Hajji a Makkah

    Gari mai cike da tantuna

    Mina wani kwari ne dake kusa da Makkah. A lokacin Hajji a kowace shekara ana kafa dubun dubatan tantuna don sauke Mahajjata a tsawon kwanakin aikin Hajji. Sauke miliyoyin Mahajjatan da kula da su na zaman babban ƙalubale a lokacin aikin Hajji a kowace shekara.

  • Tsarkake kai

    Aikin Hajji a Makkah

    Tsarkake kai

    Kafin fara aikin Hajji maza maniyata na sanya fararen tufafi wato Ihram da ya ƙunshi ƙyallaye guda biyu da najasa ba ta taɓa ba. Duk mai sanye da wannan tufafi ya shiga Harami kenan.

  • Arafat: Tudun gafara

    Aikin Hajji a Makkah

    Arafat: Tudun gafara

    Ranar Arafat na zama ƙololuwar aikin Hajji, kuma duk wanda ya rasa Arafat wato idan bai tsaya a filin Arafat ba, to ba shi da Hajji. Arafat dai na da nisan kimanin kilomita 25 gabas da birnin Makkah. A nan Annabi Mohammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi huɗubarsa ta ƙarshe. A kewayen dutsen Arafat Mahajjata na ibadodi da addu'o'i da neman gafarar Ubangiji.

  • Jifan shaiɗan a Jamarat

    Aikin Hajji a Makkah

    Jifan shaiɗan a Jamarat

    Jifan shaiɗan na daga cikin rukunan aikin Hajji. Sai dai ba wai Shaiɗan ne ake gani a wurin jifan ba, an gina wasu dogayen bango ne guda uku wanda ake jifa da ƙananan duwatsu. A da ana yawaita samun haɗura a wurin jifan kasancewa wurin ya matsu. Amma faɗaɗa Jamarat da aka yi yanzu abubuwa sun kyautatu.

  • Raba wa matalauta abin yanka

    Aikin Hajji a Makkah

    Raba wa matalauta abin yanka

    Yanka dabba na daga cikin muhimman ɓangarorin aikin Hajji. Ana wannan aikin ibada ne don tunawa da Annabi Ibrahim (Alaihis Salat was-Salam:ASW), wanda bisa bin umarnin Ubangijinsa ya nuna shirin yanka ɗansa Annabi Isma'il (ASW). Kamar a cikin littafin Bible, maimakon mutum, ana yanka dabba ne don cika wannan rukuni na ibada. Akasari ana raba naman ne ga talakawa.

  • Safa da Marwa

    Aikin Hajji a Makkah

    Safa da Marwa

    Sa'i wato tafiya tsakanin Safa da Marwa, ibada ce dake da tarihi tun a cikin Linjila. Mahajjata na kai komo sau bakwai inda suke farawa daga Safa su ƙare a Marwa. Wannan ibada na tunasarwa ga Hajar matar Annabi Ibrahim (ASW), wadda a wajen neman ruwa ga ɗanta Annabi Isma'ila ta yi kai komo sau bakwai tsakanin duwatsu Safa da Marwa, kafin Ubangiji ya nuna mata rijiyar ruwan Zamzam.

  • Ƙoƙarin taɓa Ka'aba

    Aikin Hajji a Makkah

    Ƙoƙarin taɓa Ka'aba

    Sau tari a kan samu turmutsitsi a koƙarin taɓa Ka'aba, inda wani lokaci ya kan kai ga asarar rayukan Mahajjata. Alal misali a shekarar 2006 mutane fiye da 350 suka rasu sakamakon turereniya wajen jifan Shaiɗan.

  • Jam'i

    Aikin Hajji a Makkah

    Jam'i

    Musulmi kimanin miliyan biyu da rabi daga ƙasashe daban daban na duniya su ka tafi Makka domin sauke faralin Hajji a shekarar 2011. Likitoci da ma'aikatan jiyya kimanin 20,000 suka zauna cikin ko-takwana don kula da Mahajjatan. Sojoji da 'yan sanda 100,000 suka samar da tsaro a lokacin aikin Hajjin shekarar 2011.

  • Kaɗaita

    Aikin Hajji a Makkah

    Kaɗaita

    Ga mafi yawan al'ummar Musulmi, Hajji na zama wani aikin ibada mafi muhimmanci a rayuwarsu. Sai dai ba safai a lokacin aikin Hajji mutum ke iya samun kansa shi kaɗai a wuri ba kamar wannan mutumin a kan dutsen Arafat.


    Mawallafi: Rachel Gessat | Edita: Mohammad Nasiru Awal

SHIRYE-SHIRYE

Rediyon DW koyaushe a cikin kunne

ALBISHIR: Kuna iya sauraron shirye-shiryen DW a harsunan Afirka guda shida kai tsaye (hausa, swahili, amharik, ingilishi, faransanci, harshen Portugal) a duk lokutan da aka saba. Idan sun wuce ku, kuna iya sauraren shirye-shiryen Hausa ta „Audio on demand“! Kuna iya zaben abin da za ku saurara daga jerin shafunan dake kasa.

Kuna iya tuntuɓarmu akan wannan adireshi: hausa@dw.de ko kuma ku aiko mana da gajeren saƙo akan wayarmu mai lamba: +49-173-7100428