1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages
  • Ɗauri a gidan firsina

    'Yan ci rani a Libiya

    Ɗauri a gidan firsina

    Wani sabon rahoto ya bankaɗo yadda ƙungiyoyin sojin sa kai a Libiya ke take haƙƙin baƙi. Kafin rikicin Libiya, yawan baƙi 'yan ci rani ya kai kashi ɗaya cikin uku na yawan al'ummar ƙasar. Yanzu da ƙasar ta fara sake gina kanta, ta sake zama abar sha'awa ga 'yan ci rani. Amma mafi yawancinsu na shiga hannun ƙungiyoyin 'yan banga, dake ɗaure su a sansanoni kamar wannan a Gharyam tsawon kwanaki.

  • Jiran tsammani wa Rabbuka

    'Yan ci rani a Libiya

    Jiran tsammani wa Rabbuka

    'Yan ci ranin, mafi yawansu daga ƙasashen Afirka kudu da Sahara, ana tsare su a sansanoni marasa kyau lokaci mai tsawo. Hukumar ƙasa da ƙasa ta kare haƙƙin ɗan Adam (FIDH), wadda ta wallafa rahoton, ta gano cewa halin da ake ciki a sansanoni ya ƙazanta kuma bai dace da wurin zaman ɗan Adam ba. A nan firsinoni ne a wani sansani dake birnin Bengazi suna jiran a kore su zuwa ƙasar Masar.

  • Firsinoni a teku

    'Yan ci rani a Libiya

    Firsinoni a teku

    Wani "ƙaramin gungu" na 'yan ci rani su ne waɗanda ake katse wa hanzari a tekun Bahar Rum lokacin da suke ƙoƙarin tsallakawa zuwa Turai. Suna ƙaurace wa wahalhalu da cin zali a yankin ƙahon Afirka inji Messaoud Romdhani, wanda ke cikin masu binciken. Ya ƙara da cewa suna da 'yancin samun kariya ta ƙasa da ƙasa. Waɗannan mata 'yan Somaliya an tsare su ne a teku a kan hanyar zuwa tsibirin Malta.

  • Cikin gidan kaso

    'Yan ci rani a Libiya

    Cikin gidan kaso

    Rahoton ya soki manufofin tarayyar Turai dake da nufin tsananta bincike a iyakokinta na waje domin daƙile kwararar 'yan gudun hijira zuwa yankin EU. "Dole mu yarda cewa batun baƙin haure ba na tsaro ne kaɗai ba, batu ne da ya shafi haƙƙin ɗan Adam," inji Franziska Branter wakiliyar jam'iyar The Greens a majalisar Turai. A nan wani mutum ne daga Laberiya da aka tsare a wani kurkuku da aka ware.

  • Wariyar launin fata

    'Yan ci rani a Libiya

    Wariyar launin fata

    Da akwai wani dalili da ya sa ake nuna wa 'yan Afirka kudu da Sahara wariya a Libiya. Ɗaya daga cikin jagororin sojin sa kai ya faɗa wa masu binciken cewa, "ba ma son waɗannan mutanen a nan, suna aikata laifi, suna kuma shigo mana da cututtuka." A nan 'yan gudun hijira a wani sansani a Bengazi dake ƙarƙashin kuluwar ƙungiyar agaji ta Red Crescent da kuma UNHCR.

  • Ƙwadagon dole

    'Yan ci rani a Libiya

    Ƙwadagon dole

    'Yan ci rani a sansanin Gharyan a kan hanyar zuwa ƙwadago a wata gona. Kamfanoni masu zaman kansu na ba da aiki ga 'yan ci ranin da aka tsare, ƙarƙashin wani yanayi da masu binciken suka kwatanta shi da "aikin ƙwadago na tilas." "Baƙin ba su da masaniya tsawon lokaci da za a bukaci aikinsu ko ma za a biya su," inji Genevieve Jacques ta hukumar kare haƙƙin ɗan Adam ta ƙasa da ƙasa.

  • Haƙƙin ɗan Adam

    'Yan ci rani a Libiya

    Haƙƙin ɗan Adam

    Rahoton ya ba da shawarar cewa ya kamata ƙungiyar tarayyar Turai ta dakatar da yarjeniyoyin da ƙulla da Libiya game da baƙin haure, har sai Libiya ta tabbatar da mutunta haƙƙin ɗan Adam. "Abu mafi muhimmanci shi ne kare mutanen dake shiga Libiya amma ba sa ido a kan kwararar 'yan ci rani ba," inji lauyar 'yan gudun hijira, Caroline Intrand. Wannan hoton ya nuna kason da aka tsare matan Somaliya.

  • 'Raba nauyi'

    'Yan ci rani a Libiya

    'Raba nauyi'

    'Yan ci rani a harabar sansanin Gharyan. Yayin da ƙungiyoyin sojin sa kai ke sa musu ido, hukumar ƙasa da ƙasa ta kare haƙƙin ɗan Adam ta jaddada buƙatar raba nauyi tsakanin gwamnatin Libiya, ƙungiyar EU da ƙasashe membobinta wajen tinkarar matsalar take haƙƙin ɗan Adam.


    Mawallafi: Joanna Impey | Edita: Mohammad Nasiru Awal

SHIRYE-SHIRYE

Rediyon DW koyaushe a cikin kunne

ALBISHIR: Kuna iya sauraron shirye-shiryen DW a harsunan Afirka guda shida kai tsaye (hausa, swahili, amharik, ingilishi, faransanci, harshen Portugal) a duk lokutan da aka saba. Idan sun wuce ku, kuna iya sauraren shirye-shiryen Hausa ta „Audio on demand“! Kuna iya zaben abin da za ku saurara daga jerin shafunan dake kasa.

Kuna iya tuntuɓarmu akan wannan adireshi: hausa@dw.de ko kuma ku aiko mana da gajeren saƙo akan wayarmu mai lamba: +49-173-7100428